Kungiyar War Against Injustice Ta Bukaci A Gaggauta Yin Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kano.

Spread the love

Kungiyar kare hakkin dan Adam da yaki da rashin adalci da bibiya a kan shugabanci nagari wato War Against Injustice , ta bukaci shugaban hukumar zabe ta jihar Kano da ya gaggauta yin zaben kana hukumomin Kano.

A cikin wata wasika mai shafi biyu da Kungiyar ta aike wa shugaban hukumar zabe ta jihar Kano me dauke da sahannun babban darektan Kungiyar Comr.
Umar Ibrahim Umar , ta ce ta yi hakane sakamakon hukunci da kotun kolin Najeriya ta yi na bawa kananan hukumomin yancin cin gashin kai,  da ta sarafin kudadensu wanda hukuncin ya hana wa gwamnoni ci gaba da tasarafi da kudaden kana hukumomin.

Idan za’a tuna ko a baya Kungiyar ta bukaci majalisar dokokin Kano a kan ta hana gwamnatin Kano diban kaso 70 na kudaden kananan hukumomin Kano 44 domin yin Gadar sama ta Danagundi da kuma Tal’udu.

Kungiyar ta zayyana wa hukumar zabe dalilolinta guda 6 na bukatar gudanar da zaben kanana nan hukumomin Kano,  wanda suka hada da yin biyayya ga hukuncin da Kotun koli ta yi na kwanan nan, cewa kudin tsarin mulkin kasa ya dora hukumar alhakin yi wa kananan hukumomin zabe, don haka ta sauke nauyi da ya ke kanta, bukatar tabbatar da Dimokaradiyya daga tushe, domin samar da ci gaban jama’a kamar gina asibitoci, makarantu da samar da hanyoyi, kauracewa yin asarar samun kason kananan hukumomin Kano domin gwamnati tarayya za ta iya hana kananan hukumomin Kano kasonsu na rabon tattalin arzikin kasa sakamakon ba zababbu ba ne a kai.

Saboda wadancan dalilan, Kungiyar ta nemi a gudanar da zaben cikin gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *