Kungiyar War Against Injustice Ta Gargadi Gwamnonin Najeriya A Kan Yunkurin Hana Zanga-zangar Lumana Da Ake Shirin Yi.

Spread the love

Kungiyar kare hakkin dan Adam, yaki da rashin adalci, da bibiya a kan shugabanci nagari me suna War Against Injustice ta gargadin gwamnonin Najeriya a kan kada su hana mutanen jihohinsu yin zanga-zangar lumana a kan kuncin rayuwar da ake ciki.

Wannan yana kunshe ne a cikin wata takarda me dauke da sahannun babban darektan Kungiyar, Comr. Umar Ibrahim Umar wacce aka rabawa manema labarai a ranar Talata a birnin Kano.

Takarda ta kara da cewa ba daidai bane gwamnonin su hana Yan kasa cin gajiyar hakkin da kundin tsarin mulkin kasa, da sauran dokokin duniya wanda Najeriya ta saka hannu da kuma tsarin mulkin Dimokaradiyyar ya basu na fitowa su nuna kunci da tsadar rayuwar da suke ciki.

Idan za’a tuna, Kungiyar ta sanar da shirinta na jagorantar zanga-zangar lumana a birnin Kano domin yin kira ga gwamnati tayi duba a kan halin matsi da al’umma suke ciki wanda ya janyo a hankali mutane su na mutuwa.

Sanarwar ta ja hankali jami’an tsaro a kan cewa kada su sake su tilasta duk wani umarni da gwamnonin zasu bayar game da hana zanga-zangar lumana a jihohinsu, domin doka tayi tanadin duk umarnin da gwamnonin zasu bayar, indai ya sabawa doka to kada jami’an tsaro su tilasta binsa.

Kungiyar ta tunatar da gwamnonin kasar nan cewa lokacin da aka cire tallafin Man fetur hada kansu sukayi sukaje wajen shugaban kasa suka nuna goyan bayansu kuma yanzu sunki fadar halin kuncin da al’umma suke ciki, a don haka bazasu iya hana Yan Najeriya fitowa su fadi matsin da suke ciki ba.

Kungiyar ta bukaci al’ummar Najeriya da suyi zanga-zangar cikin lumana tare da girmama dokokin kasa da Kuma hakkokin jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *