Kungiyar Yaki Da Rashin Adalaci ( WAI) Ta Gamsu Da Hukuncin Da Aka Yanke Wa Frank Geng

Spread the love

Kungiyar Kare hakkin adam da bibiya kan shugabnci nagari ( War Against Injustice) ta bayyana gamsuwar ta kan hukuncin da wata babbar kotun jahar Kano, ta yanke wa dan kasar Chaina, Frank Geng Quarong da aka Samu da laifin hallaka tsohuwar budurwarsa mai suna Ummulkursum Sani Bahari (Ummita) Tun a ranar 16 ga watan Satumba 2022.

Shugaban kungiyar kwamared Umar Ibrahim Umar, ne ya bayyana hakan a tattauna war da ya yi da jaridar idongari. ng, a ranar Talata a birnin Kano.

Kwamared Umar Ibrahim ya ce wannan abun jin dadi ne , kuma abun farin ciki , domin duk Wanda ya salwantar da rayuwar wani hukuma ba zata kyale ba, kuma yin hakan ya Kara mu su kwarin gwiwar Ci gaba da fatan samun adalci a kotunan jahar Kano.

Kungiyar ta yaba wa Kwamishinan Shari’a na jahar Kano, Barista Haruna Isah Dederi, kan tsayuwar da  ya yi Kai da fata, har saida ya tabbatar an yi adalci a wannan shari’ar.

Haka zalika ya jinjina wa bangaren Shari’a da Alkalin da ya yanke hukuncin wato mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji, da sauran lauyoyi, Yan Sanda da kuma Yan Jarida da suka bibiyi shari’ar, har zuwa wannan lokaci.

” Duk wani da yake da yunkuri ko na cin zarafin wani munsan akwai hukunci da za a yanke masa ” .

Umar Ibrahim, ya yi Kira ga gwamnan jahar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf, da ya gaggauta sanya hannu da zarar wa’adin daukaka kararsu ya Kare, don a zartar masa da hukuncin da babbar kotun jahar Kano ta yanke masa.

Idan ba a manta ba jaridar idongari.ng, ta ruwaito mu ku cewa Wata Babar kotun jahar Kano, ce ta yanke wa Frank Geng Quarong hukuncin kisa ta Hanyar rataya har sai ya daina motsi, bisa samun sa da kotun ta yi da laifin hallaka tsohuwar budurwarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *