Kungiyar Yan Kasuwar Sabon Garin Sun Zargi Wasu Jami’an Kwastam Da Yi Wa Kasuwancinsu Kanshin Mutuwa

Spread the love

Kungiyar yan kasuwa dake kasuwar Sabon Gari, a jahar Kano, sun zargi wasu wasu jami’an hukumar Kwastam da yi wa harkokin kasuwancin zagon kasa ta hanyar kama kayansu tare da sanya mu su harajin dole.

Sakataren kungiyar yan kasuwar, Nura Abdullahi, ya bayyana takaicinsa kan yadda jami’an kwastam din ke yiwa kasuwancin su kanshin mutuwa.

Ya kara da cewa suna kama motacin kayansu a cikin gari ne, sannan su bukaci sai an biya kudi kafin su saki motar, dadi da barazar da suke yi mu su cewar wajibi ne a bayar da kudin a hannu ba ta banki ba kuma idan wa’adin da suka ba su ya cika za su mika motar zuwa ofishin su a Abuja.

Yan kasuwar sun ce yanzu haka sun fara rasa abokan kasuwancinsu da suke zuwa daga sauran jahohi , sakamakon kama mu su kaya da ake yi, duk da cewar ba daga kasashen waje suka siyo su ba.

Kakakin hukumar Kwastam reshen jahar Kano Sa’id Nuraddin, ya musanta zargin tare da yin kira ga yan kasuwar su kai mu su korafi zuwa ofishinsu, don kamo baragurbin jami’an kwastam din.

A karshe yan kasuwar sun yi bukata mahunkunta da su shiga cikin lamarin don yi wa tufkar hanci, na samar mu su kwanciyar hankali na gudanar da kasuwancinsu ba tare da razani ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *