Kungiyoin daliban jahar Bauchi sun bukaci kwamishinan yan sandan jahar ya dauki mataki kan masu far mu su da makami

Spread the love

Kwamishinan yan sandan jahar Bauchi CP Auwal Musa Muhammed, ya karbi bakuncin shugabannin kungiyoyin dalibai na jahar da suka hada da NUBAS da kuma SUG, a ofishin sa dake shelkwatar rundunar yan sandan jahar.

Ziyarar ta su na zuwa ne kwanaki kadan, da ake zargin wasu da ba a san ko su waye ba, da suka yi yunkurin kwace jakar hannun wata dalibar mai suna Philomena Ahobee dake karatu a makarantar Abubakar Tatari Polytechnic, inda saurayin ta mai suna Agbaidu Joseph dalibi a jami’ar Abubakar Tabawa Balewa , ya kai mata daukin gaggawa domin tsira da jakar da kuma wayar ta sai dai wanda ake zargi ya caka masa wuka a kirjinsa.

Mai Magana da yawun rundunar yan sandan jahar Bauchi SP Ahmed Muhammad Wakil , ya ce bayan faruwar lamarin an garzaya da matsahin zuwa asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) Bauchi inda likita ya tabbatar da ya mutu.

Shugabannin daliban sun yi kira ga daliban jahar su kwantar da hankalinsu , domin zanga-zanga ba zata haifar da da mai ido ba sai ma kara dagula lamura, domin duk abinda ya faru akwai hanyoyin da ake bi domin magance matasalar.

Shugabanin daliban sun gabatar da wasikar neman Karin jami’an tsaro ga kwamishinan yan sandan jahar Bauchi dan sanya ido a unguwannin da dalibai ke zama.

Kwamishinan yan sandan jahar Bauchi CP Auwal Musa Muhammed , ya bas u tabbacin kara jami’an yan sanda a yankin dan kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyin su.

Dalibin dai sun koka da yadda wasu batagari ke yunkurin hana su zaman lafiya, sakamakon yadda ake far musu da makamai dan kwace wayoyin su ko kuma yi mu su sata cikin dare, wanda hakan barazana ce ga karatun su da lafiyar su.

Kafin dai kwamishinan yan sandan ya fara jawabi sai dai ya yi shiru na minti daya domin girmama wag a dalibin da ya rasa ransa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *