Kungiyoyin Kwadagon Nigeria Sun Watsi Da Karin Albashin Da Gwamnati Ta Yi Wa Ma’aikata

Spread the love

Ƙungiyar ƙwadago ta TUC a Najeriya ta yi watsi da ƙarin albashin da gwamnatin tarayyar ƙasar ta sanar a ranar Talata, kwana ɗaya gabanin bikin ranar ma’aikata ta duniya.

A jiya ne wata sanarwa wadda ta samu sa hannun shugaban hukumar kula da albashin ma’aikata ta Najeriya, Ekpo Nta, ta bayyana cewa an yi ƙarin kashi 25 zuwa 35 cikin ɗari a kan albashin ma’aikatan gwamnati.

Hakan ya nuna cewa mafi ƙarancin albashi zai koma kimanin naira 37,000 daga naira 30,000 da ake da shi a baya.

Sai dai a tattaunawar sa da BBC, sakataren ƙungiyar ƙwadago ta TUC, kwamared Nuhu Abbayo Toro ya ce ba da sanin ƙungiyoyin ƙwadago aka yi ƙarin albashin ba kuma ba su amince da shi ba.

Toro ya ce “abin da dokar ƙasa ta ce shi ne sai an zauna an tattauna an yi yarjejeniya an samu matsaya kafin a amince da albashi mafi ƙanƙanta”.

Ya ƙara da cewa “ba daidai ba ne shugaban ƙasa ya furta cewa ya yi ƙarin albashin ma’aikata alhali akwai kwamitin da ke aikin samar da sabon albashi mafi ƙaranci”.

Shi ma shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC, Joe Ajaero a wata tattaunawa da kafar talabijin ta Channels da safiyar Talata ya ce “sanarwar da aka bayar an yi ta ne da wata manufa domin kuwa babu wani ƙarin albashi da aka yi”.

A watan Janairu ne Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ƙaddamar da wani kwamiti wanda zai duba tare da yanke shawara kan ƙarancin albashin ma’aikata a ƙasar.

An ɗauki matakin ne bayan barazanar da ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasar suka yi kan cewa za su tsayar da lamurra cak a ƙasar har sai gwamnatin tarayya ta samo mafita game da matsin rayuwa da ma’aikatan ƙasar ke fuskanta.

Al’ummar Najeriya na fuskantar tashin farashin kayan masarufi tun bayan da shugaban ƙasar ya sanar da janye tallafin man fetur da gwamnati ke bayarwa a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *