Kungiyoyin ma su bukata ta musamman karkashin kungiyar JONAPWD reshen Jihar Kano, sun nesanta kan su daga zanga-zanga tare da taron manema labarai da aka yi a matsayin Kungiyar Hadin Gwiwar masu Bukata ta musamman a jihar.
Hadin Gwiwar Kungiyoyin PWDs sun samu labarin wannan zanga-zanga da kuma taron manema labarai da wasu mutane suka shirya don matsa lamba ga gwamnatin Jihar Kano Ƙarƙashin Jagorancin Abba Kabir Yusuf kan kafa hukumar kula da masu bukata ta musamman a jihar.
Muna nisantar kanmu gaba daya daga wannan taron manema labarai da zanga-zangar da ake zargin masu bukata ta musamman sun shirya ba mu san da zanga-zangar ba, kuma ba mu da hannu a cikinta!
Maimakon shirya zanga-zanga, mun zabi amfani da hanyoyin sadarwa na kai-tsaye da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta tanada, inda ake sauraron korafe-korafenmu.
Hadin Gwiwar Kungiyoyin PWDs da shugabancin JONAPWD suna son jaddadawa manyan nasarorin da aka samu wajen inganta rayuwar mutanen da ke da bukata ta musamman karkashin jagorancin Mai Girma Abba Kabir Yusuf.
Tallafin Kai Tsaye Daga Gwamnati:
A cikin kwanaki 100 na farko na mulkinsa, gwamnatin Jihar Kano ta bayar da gagarumin tallafi ga PWDs, wanda ya hada da:
Gwamnati ta tallafa wa bikin Ranar masu bukata ta musamman ta Duniya ta 2024 da kuma Ranar Kariya Ga Mutanen Da Ke Da Rauni Na Kashin Baya na shekarun 2023 da 2024.
Duk da cewa muna goyon bayan kafa hukumar kula da masu bukata ta musamman, muna jaddada cewa Jihar Kano ita ce mafi da cewa da PWDs a Najeriya kuma tana kan hanyar aiwatar da manufofi na ci gaban PWDs.
Muna godiya ga gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Mai Girma Injiniya Abba Kabir Yusuf kan irin karfafa gwiwa da shigar da PWDs a cikin ajandar ci gaban jihar.
Muna kira ga dukkan mambobin Hadin Guiwar Kungiyoyin PWDs na Kano, JONAPWD da jama’a baki daya, su nisanci duk wata zanga-zanga da ake yi da sunan kare hakkokin PWDs a Jihar Kano, domin wannan ba hanyar mu ba ce.
Sa hannu:
Musa Muhammed Shaga