Kura ta tsere gandun dajin Jos

Spread the love

Ana zaman fargaba a yankin Dong na Jos ta arewa a jihar Filato bayan da wata kura ta kuɓuce a gandun daji.

Dabbar ta dawa hatsibibiya ta tsere ne a ranar Lahadi kamar yadda gwamnatin Filato ta tabbatar wa jaridar Punch.

Lamarin ya razana mazauna yankin da kuma jihohi makwabta.

Gwamnatin jihar ta bukaci mutane su kwantar da hankalinsu domin an shiga farautar kurar kafin ta yi ta’adi.

Wasu dai na cewa tsananin yunwa ce ta tilastawa kurar tserewa, wani abin da hukumomin jihar Filato suka musanta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *