Kwalejin Koyar Da Aikin Gona Ta Audu Bako Ta Musanta Zargin Kin Bin Umarnin Gwamnatin Kano.

Spread the love

 

Kwalejin koyar da aikin gona ta Audu Bako College of Agriculture Danbatta (ABCOA Danbatta), ta musanta labarin cewa makarantar ba ta bin umarnin gwamnatin jihar kano.

Shugaban Makarantar, Farfesa Muhammad Audu Wailare, ne ya bayyana hakan a yayin ganawar sa da manema labarai a ofishin sa, inda ya ce zargin da shugaban ƙungiyar malaman Kwalejin Kimiyya da fasaha ta kasa reshen Arewa Maso Yamma, Dakta Abdul Aziz Badaru ya yi ba gaskiya ba ne.

A cewar Farfesa Wailare, “Zargin Dakta Abdul Aziz Badaru ba komai ba ne illa yunkurin bata sunan makarantar mu, la’akari da yadda ya ke yada Labaran Kanzon Kurege game da dakatarwar da aka yiwa wani malami mai suna Malam Ahmad, bisa zargin sa da dukan wani malami a Idon Jama’a”.

Wailare ya kara da cewa hakan ne ya sanya shugaban waccan Kungiya ya ke amfani da kafafen yaɗa labarai wajen yada cewa sun bijirewa umarnin gwamnatin Kano, duk da makarantar da kuma shugaban Ma’aikata na jihar ne suka dauki matakin dakatarwar.

A ƙarshe ya ce a tsawon shekarun da ya dauka a matsayin Shugaban Makarantar babu wata gwamnatin da ta bawa makarantar kulawa ta musamman irin gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusif.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *