Kwamishina ya yi murabus kan ƙarbar belin dillalin ƙwayoyi a Kano

Spread the love

Kwamishinan sufurin jihar Kano da ke arewa maso gabashin Najeriya ya ajiye muƙaminsa kan zargin alaƙarsa da mutumin da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a jihar.

Gwamnatin jihar Kano ce ta sanar da murabus ɗinsa a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Laraba.

Ibrahim Ali Namadi ya ajiye muƙaminsa na kwamishina ne bayan gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin binciken zarginsa da hannu a belin Sulaiman Aminu Danwawu, wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a jihar.

Batun belin Danwawu da ake zargin da hannun kwamishinan, ya ja hankalin jama’ar Kano da ma Najeriya.

“Kwamishinan ya ce ya yanke shawarar yin murabus ne saboda buƙatar al’umma da kuma tasirin al’amarin.”

“A matsayin mamba na wannan gwamnati wanda ke kan gaba wajen yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, mataki ne da ya dace na ɗauka,” a cewar sanarwar.

Sai dai a sanarwar, Kwamishinan ya ci gaba da kare kansa a matsayin marar laifi tare da nisanta kan shi da zargin da ake masa.

“Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus ɗin kwamishinan, tare da yi masa fatan alheri,” kamar yadda Sunusi Bature Dawakin Tofa ya shaida wa BBC.

Ya kuma ce gwamnatin Kano ta bayyana matakin kwamishinan a matsayin wani muhimmin cigaba a ƙoƙarin gwamnati wajen tabbatar da gaskiya da kuma riƙo da amanar al’umma.

A ranar Litinin ne kwamitin binciken badaƙalar belin Danwawu, ƙarƙashin jagorancin Barrister Aminu Hussaini ya miƙa rahoton bincikensa ga sakataren gwamnatin jihar.

Babu dai cikakken bayanin abin da rahoton ya ƙunsa, amma a hirarsa da BBC, mai magana da yawun gwamnan jihar ya ce kwamitin ya gano abubuwa kusan guda tara.

Ya ce gwamna Abba Kabir zai yi nazari game da rahoton kafin ɗaukar mataki na gaba.

Sai dai gwamnatin ba ta bayyana ko matakin da za ta ɗauka ba zai shafi Ibrahim Ali Namadi bayan ajiye muƙaminsa na kwamishinan sufurin jihar Kano.

Zargin Namadi da ƙarbar belin Danwawu, mutumin da ake zargi da dillancin miyagun ƙwayoyi, ya janyo zazzafar muhawara a Kano da Najeriya inda wasu ke ganin bai kamata mutum mai matsayi irin na kwamishina ya karɓi belin mutumin da ake zargi da taimakawa masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a jihar ba.

Lamarin da ya sa wasu al’ummar jihar ke ta kiran lalle sai gwamnati ta ɗauki mataki a kan kwamishinan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *