Rundunar yan sandan jahar Kano ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda yan uwan wata mara lafiya suka farwa wani likita a asibitin kwararru na Murtala Muhammed dake jahar.
Lamarin ya faru a ranar 28 ga watan Janairu 2024, inda ake zargin yan uwan mara lafiyar da ta rasu , sun kai farmaki ga likitan mai suna Shehu Usman Abdulwahab, dake aikin a sashe kula da masu haihuwa.
Iyalan yan sanda 88 da suka rasu sun karbi Chekin kudi sama da N40m a Kano.
Yan sanda sun gurfanar da wani mutum bisa zargin yaudara da sace Adaidaita sahu a Kano
Mukaddashin mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar Kano, ASP Abdullahi Hussaini ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aike wa da manema labarai.
Ya ce bayan samun rahoton ne, kwamishnan yan CP Muhammed Usaini Gumel, ya tura tawagar jami’an yan sanda inda suka kai daukin gaggawa .
Sanarwar ta kara da cewa, kwamishinan yan sandan ya kai ziyara asibitin Murtala Muhammed, inda ya gana da mahukuntan asibitin tare da tabbatar mu su cewa rundunar ta fara gudanar da bincike, tare da daukar matakan kara jami’an tsaro, don kare rayukan al’umma da kuma jami’an kiwon lafiya.
Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya kara da cewa rundunar ba zata amince da duk wani nau’in cin zarafi ga ma’aikatan kiwon lafiya da suke aiki don ceto rayuka da kuma marasa lafiya.
Rundunar ta yi kira ga masu korafi kan jami’an kiwon lafiyar su daina daukar doka a hannun su, su dinga kai korafinsu ta hanyoyin da suka dace don daukar mataki tare da warware sabanin da ya shiga tsakani.