Kwamishinan yan sandan Kano CP M.U.Gumel, ya ce idan ya samu labarin yan Daba na tayar da zaune tsaye a jahar baya jin dadi a zuciyarsa.

Spread the love

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya bayyana cewa duk lokacin da ya samu labarin cewar yan Daba a fadin jahar Kano suna tada zaune tsaye ya kanji babu dadi a ziciyarsa.

Wannan dai na zuwa ne sakamakon kokawar da al’ummar Unguwar Madigawa dake yankin karamar hukumar Dala ke ci gaba da yi , inda gungun wasu yan daba ke yi mu su fashin kayayyakinsu tare da yunkurin raunata su da makamai.

Alhaji Tijjani Usama Dattijo ne da ke Unguwar Madigawa, ya shaida wa Idongari.ng, cewar a ranar Alhamis da misalin karfe 8:00pm na dare Yan Dabar sun shiga shagon Dansa dake yin sana’ar Chajin Waya, da Rijista, inda suka kai masa sara da makami, sannan suka dauki wayar Salula 1 da kuma kudi Naira dubu dari biyu 200,000.00.

Dattijon ya kara da cewa akwanakin baya yan Dabar sun zo tare da fasa Motocin jama’a , inda al’ummar yankin suka tattauna domin magance matsalar kuma abun ya lafa sai dai yanzu sun kara dawo wa.

 

” Akwai wani lauya ya sanarwa da DPO na yankin, inda shi kuma DPO ya tura jami’an yan sanda domin kare rayukan al’umma da dukiyoyin su.

 

Al’ummar Madigawar sun zargi wasu da rashin tsawatar wa yayan su , domin sun ce an san wasu dake aikata wannan laifi, inda suke zuwa cikin dare dauke da makamai su kusan, sama da 100, har suke fasa shagunan jama’a su sace kayan.

 

Sai dai kwamishinan yan sandan Kano CP Muhammed Usaini Gumel , ya ce baya jin dadin yadda yan Daba ke aikata laifuka, inda ya tabbatar da cewa za su dauki matakin da ya dace, domim a wannan lokaci ya samu labarin faruwar lamarin, domin babu wani daga cikin jagorin unguwar da ya kawo mu su korafi.

 

Ya kuma kara da cewa, suna aiki sa sauran hukumomin tsaro dan ci gaba da wanzar da zaman lafiya, ya kuma kwantar da hankulan jama’ar jahar Kano da cewa za su bincika faruwar lamarin dan daukar matakin da ya dace.

 

Al’ummar jahar Kano sun yaba da matakan da kwamishinan yan sandan Kano CP Muhammad Usaini Gumel , yake dauka na dakile aiyukan batagari a jahar Kano baki daya.

Ko a watannin baya wasu gungun yan daba sun ajiye makaman su cikinsu harda wadanda suka yi kaurin suna a sassan jahar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *