Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammad Usaini Gumel, ya gudanar da wata ganawa ta musamman da shugabannin kafafen yada labari dake jahar, don ci gaba da karfafa mu su gwiwa kan gudunmawar da suke bayar wa dan tabbatar da tsaro a jahar Kano.
Kwamishinan yan sandan jahar Kano, Muhammad Usaini Gumel, ya bayyana cewa, tunda ya zo jahar Kano watanni 7 da suka gabata ya samu hadin kan kafafen yada labaran dari bisa dari, inda ya gode mu su da jajircewarsu a koda yaushe.
Ya kara da yin kira ga kafafen yada labaran su ci gaba da ba su gudunmawa musamman a wannan lokaci da aka zo karshen shekara, da kuma batun fara sauraren shari’ar zaben gwamnan Kano a kotun koli da za a yi a ranar Alhamis 21 ga watan Disamba 2023.
Sai dai kwamishinan yan sandan ya bayyana takaicinsa kan yadda wasu daga cikin masu amfani da shafukan sada zumunta suke rubuta abubuwan da ke tayar da hankulan al’umma, kan hakanne ya dada yin kira ga Manema labarai su kaucewa yin dogaro da abubuwan da za su gani a shafukan sada zumunta.
Ya ce duk wanda yaji wani labari a kafafen yada labarai mai sauraro yana yadda da su dari bisa dari dan haka a dinga tantance dukkanin abubuwan da aka gani kafin a yada.
CP Gumel ya ce, irin wadancan labarai marasa tushe da wasu ke yadawa a shafukan sada zumunta suna haifar da babbar matsala, inda wasu ke tada hartsigi , sace-sace kayan jama’a da dai sauransu.
“wannan jaha ta mu ce ya kamata mu tsaya mu tsare mutuncin ta, mu tsare mutuncin kowa da kowa a cikin.
Yansanda sun kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja
Yansanda sun kama mutum takwas da suke zargi da sace É—aliban Ekiti
Ya tabbatarwa da mutanen jahar Kano, cewa ba sa fuskantar wata barazana ta rashin tsaro kowa ya kwantar da hankulan sa , kuma a ci gaba da gudanar da harkokin yau da kullum kamar yadda aka saba ba tare da jin wata fargaba ba.
Ya kara da ce wa , ba iya shugabannin kafafen yada labarai suka kira ba, koda abaya sun gayyaci shugabannin jam’iyyun siyasar NNPP da APC dake jahar , tare da sanya hannu kan yarje-jeniyar zaman lafiya da kuma jan kunnen magoya bayansu karsu tada hargitsi.
Taron ya samu halattar shugabannin kafafen yada labarai, Telabijin da wasu shahararun Jaridun yanar gizo dake fadin jahar.
Shugabannin kafafen yada labaran sun yi maraba da tattaunawar da kwamishinan yan sandan ya yi da su , inda suka yi alkawarin ci gaba da bayar da gudunmawa a koda yaushe.
IDONGARI.NG