Kwamishinan Yan Sandan Kano CP Muhammed.U. Gumel Ya Yi Ganawar Sirri Da Manyan Jami’an Yan Sandan Jahar

Spread the love

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya yi wata ganawar sirri da manyan jami’an yan sandan jahar da kuma baturan yan sanda, don kara sanya ido, kan zirga-zirgar ababen hawa da fadada sintiri don tabbatar da tsaro a fadin jahar.

Ganawar sirrin ta gudana, ajiya juma’a a ofishin kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, kamar yadda mai magana da yawun rundnar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ce, an tattauna don kara yawan jami’an yan sandan, a wuraren taruwar al’umma musamman na ibada da sauran wuraren harkokin yau da kullum.

Haka zalika rundunar yan sandan jahar, ta gargadi batagari dake yunkuri aikata laifuka, musamman a wannan wata na Ramadan, da su kuka da kansu domin jami’an yan sandan sun yi shirin kawar da duk wani batagari da yake yunkurin tayar da hankulan al’umma.

Kwamishinan yan sandan CP Gumel, ya ba wa al’ummar jahar tabbacin ci gaba da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu , inda ya bukace su da su ci gaba da ba su hadin kai , wajen bin dokar tuki , da kara sanya ido, don basu sashihan bayanai kan masu kunnen kashi.
Lambobin karta kwana
08032419754, 08123821575, 09029292926, or
Facebook: Kano State Police Command
Twitter: Kano State Police Command (@KanoPoliceNG)
Instagram: Kano State Police Command.

Yan Sanda Sun Cafke Matar Auren Da Ake Zargi Da Daukar Hayar Matasa Don Su Hallaka Mijinta A Kaduna

An kashe sojojin Najeriya 15 a Delta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *