Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya ba wa al’ummar unguwar Sheka a karamar hukumar Kumbotso, awanni 12 su kawo sunayen matasan da ake zargin sun addabi yankin da fadace-fadacen daba da tsallaka gidajen mutane da dai sauran laifuka.
Kwamishinan yan sandan ya bayyana hakan ne a wajen taron magance matsalolin da suka addabi Sheka da kewayensu, Wanda Mataimakin kwamishinan yan sandan jihar Kano, Mai kula da area command ta Tarauni, ACP Yusha’u Mas’ud ya wakilta a yau Laraba.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa, ya ce an tattauna batutuwa masu muhimmanci musamman abinda ya shafi tsaro, tare da gano cewar Matsalar ta na cikin al’ummar.
” Kowa ya na da rawar zai taka don ganin an magance matsalar” SP Abdullahi Kiyawa “.
Haka zalika al’ummar unguwar sun Yi wa Rundunar alkawarin kawo sunayen dukkan wadanda ake zargi da siyar da kayan maye ko fadan Daba don tsaftace Sheka da kewayenta daga harkar dabar.
Shugaban kungiyar aikin tsaro da al’umma PCRC na Sheka , Aminu Magaji, ya bayyana cewa Taron ya kara wayar da kan mutane ta hanyar bayar da Shawarwarin da suka dace.
An shirya Taron karkashin jagorancin Kwamishinan yan sandan jihar Kano, Inda ya samu halattar masu ruwa da tsaki da baturen Yan Sanda da sarakunan gargajiya da sauran al’umma.
A makon da ya gabata ne aka samu hatsaniyar fadan daba tsakanin wasu matasan sheka Gidan Kaji da kuma Sheka bayan Makaranta da hakan ya Sanya firgici ga jama’ar yankin.
Tuni dai Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wasu daga cikin matasan da ake zargi da tayar da hankalin al’umma, kamar yadda kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar.