Kwamishinan Yan Sandan Kano Ya Bada Umarnin Ci Gaba Da Zaman Tattaunawa Da Masu Ruwa Da Tsaki Don Samun Hadin Kan Al’umma.

Spread the love

 

Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta bukaci al’umma su ci gaba da ba wa Rundunar hadin Kai da sauran hukumomin tsaro, da bayanan sirri don dakile aiyukan batagari.

Kwamishinan Yan Sandan jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, wand ya samu wakilcin Area Kwamandan Dala ACP Nuhu Mohammed Diggi, ne yabayyana hakan a wajen Taron wayar da kan jama’a, da aka gudanar , biyo bayan Samun rahotannin aiyukan Daba , a unguwannin , Kwanar Goda , Sheshe, Rimi-Asibiti, da sauran wurare, dake karamar hukumar Birnin Kano, don lalubo bakin zaren magance matsalar.

Sanarwar Mai dauke da sa Hannun Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta ce kowa yana da gudunmawar da zai bayar kan sha’anin tsaro.

Taron ya hadar da masu ruwa da tsaki na yankunan da lamarin ya shafa, da suka hada da masu rike da masarautun gargajiya, kwamitin aikin tsaro da al’umma PCRC, bijilanti, Yan Sandan Sarauniya da sauran masu ruwa da tsaki na yankin Mandawari, Sheshe, Kwanar Goda da kuma Jakara.

Sauran wadanda suka halacci zaman tattauna da al’ummar sune, ACP Manmir Madugu, Wakilin Fuskar Gabas, Alhaji Faruk Abdullahi da babban mataimaki ga Gwamnan Kano, kan yada labarai Alhajiji Nagoda,Malaman Addini da dai sauran su.

An tattauna muhimman batutuwan yadda jama’a da masu ruwa da tsaki, za su dinga bayar da bayan sirri ga hukumomin tsaro don dakile aiyukan batagari.

A karshe kwamishinan yan Sandan ya umarci mataimakansa da baturen Yan Sanda, da su ci da fadada Sintiri a lungu da sako da kuma ganawa da al’umma don tabbatar da bin doka da oda.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *