Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta umarci baturan ƴan sanda a faɗin jihar Kano, da su riƙe duk wanda yazo karɓar belin ƴan fashi da makamin da ta kama na yankin Ɗorayi ƙarama.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Muhammad Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan yayin taron magance matsalar yan fashi dake faruwa a unguwar Dorayi Karama, da ya gudana da yammacin yau Alhamis.
Rundunar ƴan sandan ta jihar Kano ta kuma musanta wani bidiyo dake ya wo a shafukan sada zumunta dake nuna cewar ana cakawa wani matashi wuka a unguwar ta Dorayi Karama, wanda ta ce bidiyon ba gaskiya bane.
A nasa jawabin kwamnadan bijilanti na jihar Kano Shehu Muhammad Rabi’u, cewa ya yi mas u bibiyar waɗanda aka kama da zargin aikata laifuka kafin kammala bincike,sai wasu daga cikin iyaye suka garzaya wajen yan sanda don karbar dansu.
Da yake nasa jawabin dagacin Dorayi Karama Shehu Umar Sani, ya ce za su bayar da duk wani hadin kai da rundunar ƴan sandan take buƙata wajen kamo duk wanda yake cikin ƴan daba ko fashi da makami.
- Sojojin Najeriya sun kashe ‘ƙasurgumin ɗan fashi’ Junaidu Fasagora
- Jami’ar Khalifa Isiyaka Rabi’u, Ta Yaba Wa Kwamishinan Yan Sandan Jahar Kano
Rundunar ƴan sandan ta kuma ƙara da cewa za ta fara aikin kota kwana a yankin na Ɗorayi, tare da neman haɗin kan sauran jami’an tsaro dan tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin da ma na jihar Kano baki ɗaya.
A ƴan tsakanin nan ne dai wasu rukunin matasa suka addabi al’ummar yankin na Ɗorayi, inda aka zargi sun yi kan mai uwa da wabi akan mutane da sara, tare da ƙwacen wayoyin al’umma da sauran kayayyaki ma su daraja.