Kwamishinan Yan Sandan Kano Ya Nemi Hadin Kan Kafafen Yada Labarai Don Wanzar Da Zaman Lafiyar Jahar.

Spread the love

 

Kwamishinan Yan Sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ya bukaci kafafen yada labarai , su rinka yin taka tsantsan wajen bayar da rahotanninsu ,musamman wadanda Suka shafi masarautar Kano, don kauce wa yada labaran karya, da ka iya haifar da rudani da rashin zaman lafiyar jahar.

Kwamishinan Yan Sandan ya bayyana hakan ne a wajen taron da ya jagoranta, tare da wakilan kafafen yada labaran jahar Kano, Wanda aka gudanar a shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai Kano.

KaKakakin rundunar Yan Sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin Wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, inda Kwamishinan ya ce kafafen yada labarai, suna da rawar da za su taka, don kaucewa yada labaran karya da ka iya haifar da rashin fahimta da kuma wargaza zaman lafiyar Kano.

Haka zalika kwamishinan Yan Sandan, ya yaba wa Shugabannin kafafen yada labaran jahar, bisa hadin Kai da goyon bayan suke bayarwa a koda yaushe .

Shugannin kafafen yada labaran , sun yaba wa Kwamishinan Yan Sandan, bisa kokarin da yake yi, wajen wanzar da zaman Lafiya a jahar, tare da yin alkawarin ci gaba da tantance dukkan wani labari Kafin a yada shi zuwa ga al’umma don gudun yin kitso da kwarkwata.

A karshe CP Muhammed Usaini Gumel, ya ce aikin jarida , bai tsaya iya bin ka’idojin aike wa da rahotanni  ba, harma da kiyaye yin duk wani  abu da  zai iya kawo rudani, don samun hadin kai da zaman Lafiya mai dorewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *