Kwamishinan Yan Sandan Kano Ya Yi Bikin Cika Shekara Guda A Ofis Tare Da Bayyana Nasarorin Da Aka Samu

Spread the love

Kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ya yi bikin cika shekara guda a ofishinsa dake shelkwatar rundunar, a matsayin kwmaishinan yan sandan jahar na 45.

Kwamishinan yan sandan ya shiga ofis a ranar 2 ga watan Mayu 2023, inda a yau Alhamis 2 ga watan Mayun 2024 yake cika shekara daya.

CP Gumel, ya ce lokacin da ya kama aika a jahar Kano, ya tarar da matsalar Yan Daba wadanda suke yawo akan Titina suna shaye-shaye , Fashi da makami har suka hana al’ummar jahar Rintsawa.

Amma an samu nasarar kawo karshen batagarin a sassan birnin, bisa jajircewar jami’an yan sandan , da sauran hukumomin tsaro da kuma hadin kan da al’umma suke ba su akoda yaushe.

Jaridar idongari.ng, ta ruwaito cewa, yan Daba 623 ne suka tuba tare da ajiye makamansu, bayan kama jagorin yan Dabar da yanzu haka suke gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya.

Kwamishian yan sandan ya kara da cewa, cikin shekara guda sun kama wadanda ake zargi da aikata laifuka sama dubu 3,000, kuma tuni an gurfanar da su a gaban kotuna daban-daban.

Cikin wadanda aka cafke sun hada da yan fashi da makami 337, ma su garkuwa da mutane 66, Dilolin kwaya 90, barayin Motoci 83, Barayin Adaidaita sahu 62, barayin babura masu kafa biyu 86.

Sauran sune Yan Daba 2,101, barayi 200, Yan Damfara 61 da kuma masu gudanar da hada-hadar kudaden waje ba bisa ka’ida ba.
Haka zalika rundnar yan sandan ta samu nasarar tseratar da mutane 29, da aka yi garkuwa da su tare da hada su da danginsu sai kuma mutane 65 da aka ceto bayan an yi safararsu domin kai su kasashen ketare.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Muhammed usaini Gumel, ya ce sun kwato bindigu kirar AK-47 Rifles 1, SMG rifle 3, Barretta Pistol 1, Anti- Riot Gunner 8, Double barrel 2, Makarov Pistol 5.

Sauran sun hada da bindigu kirar gida 54, bindigar harbin tsuntsaye 44, bindigar wasan Yara 14 sai harsasai da kuma kwanson harsasi.

An kuma kwato baburan sata 116, Adaidaita sahu 84, Motoci 215, wayoyin sata 3,079, jabun magani 990, shanun sata 159 da kuma Tumaki 105.

CP Muhammed Gumel , ya kara da cewa sun kwato buhunan tabar wiwi 74 da sauran miyagun kwayoyi kamar Solusho 2,371, wukake 2,145, Adduna 108, ATM 2,823, Atamfofi 4,026.

Kwashinan ya godewa Allah bisa yadda aka samu daidaito tsakanin Manoma da makiyaya a karamar hukumar Makoda, inda ya shafe kusan shekaru 40 da kuma yadda aka gana da al’ummar Gaya bayan samun sabanin siyasa tsakanin APC da NNPP har aka jiwa wasu raunuka.

Sai kuma tattaunawar da aka yi da mutanen Kwanar Dangora, sakamakon barazanar satar mutane da aka fuskanta abaya.
A karshe CP Gumel, ya godewa kungiyar PCRC, kungiyoyin al’umma, kungiyoyin matasa, Yan sandan Sa kai, Vigilanti, AMG Fondation, YoSPIS, NUJ, Kanywood, Tik-tickers.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *