Kwamishinoni Mata Na Arewacin Nigeria Sun Yi Taro A Kaduna Kan Matsalar Tsaro Da Mata da Kananan Yara Ke Fuskanta.

Spread the love

Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna da wasu kwamishinoni mata na jihohin arewacin Nigeria ,sun Yi wani zama na musamman akan tabarbarewar tsaro da zaman lafiya wanda ya shafi mata, kananan yara harma da masu bukata ta musamman.

Kwamishinar ma’aikatar mata da jin kai ta jihar Kaduna, Hajiya Rabi, ce ta tarbi kwamishinonin da suka halacci zaman taron a wani babban dakin taro a jihar Kaduna.

Wanda UN women da UNDP suka dauki nauyin gudanar da taron a jihar kaduna, a karshe dai an cimma matsaya akan kowacce jaha za suje su aiwatar da zama na musamman da mata da kananan yara da masu bukata ta musamman domin wayar da kan su tare da sanarwa da gwamnonin su cewar duk wani zama da za a yi na samar da tsaron cikin gida ya kamata a shigar da ma’aikatar mata domin sune wadanda matsalolin sukafi shafa kai tsaye, tare da Nemo hanyoyin magance matsalolin.

Ana ta bangaren Kwamishinar ma’aikatar mata, kananan yara da masu bukata ta musamman ta jahar Kano , Hajiya Aisha Lawan Saji rano, wadda ta halarci taron inda ta bayyana shirin da suka yi na tunkarar kalubalen da mata suke fuskanta ta bangaren tsaro da inganta zaman lafiya a tsakanin Al’umma.

A karshe dai, ta lashi takobin isar da wannan gagarumin sakon ga mata, kananan yara da ba masu bukata ta musamman a jihar kano domin daukar matakin gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *