Gamayyar kungiyoyi ma su zaman kansu na jahar Kano, sun bayyana cewa har yanzu, Ambasada Ibrahim Waiya, shi ne shugabansu, bayan fitar wata sanarwa da kwamatin amintattun kungiyoyin ya bayyana dakatar da shi.
Sanarwar dakatarwa mai dauke da sa hannun sakataren kwamitin Amintattun, Hamisu Isah Sharifai, ya ce an dakatar da Waiya, tsawon shekara guda.
Sai dai mataiamki na musamman ga, Ambasada Ibrahim Waiya, kan kafofin yada labarai, Bashir A. Bashir, ya bayyana cewa wasu ne kawai da ba sa kishin jahar Kano, ne ke kokarin tayar da tarzoma bisa ra’ayin kashin kansu wanda ba zai haifar da, da mai ido ba.
Bashir, ya kara da cewa kwamitin amintattun bashi da hurumin dakatar da Waiya, inda ya bukaci shugaban amintattun ya fito ya baranta kansa kan fitar da takaddar , tunda batun yana gaban kotu.
Sanarwar ta yi kira ga mambobin gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu na jihar Kano da suyi watasi da sanarwar tare da jiran me kotu zata faɗa a mako mai zuwa.
- Majalisar dattawa ta amince Tinubu ya ciyo bashin naira triliyan 1.77
- Ba mu ce ba za mu goyi bayan Tinubu ba – ACF