Kwamitin Binciken Tsohuwar Gwamnatin Kano Ya Fara Zama.

Spread the love

Kwamitin binciken da gwamnatin Jahar Kano, ta kafa domin bincikar tsohuwar gwamnatin Jahar karkashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya Fara zama, don karbar karbar korafe-korafe , kan rashin bin ka’ida Wajen yin tasarifi da dukiyar gwamnati.

Kwamitin karkashin jagorancin mai Shari’a Justice Faruk Lawan, na babbar katun Jahar Kano mai lamba 3, dake zaman ta a sakatariyar Audu Bako.

Kwamitin mai mambobi 12, inda Justice Faruk Lawan yake jagorantar kwamitin, sai kuma sauran mabobin da suka hada da Barista Abdulkarim Kabir Maude, Hamza Madaki, M.H. Gano, Architec Ibrahim Yakubu MD KNUPDa, CSP Salisu Muhammed Wakilin Rundunar yan sanda ta kasa, Ibrahim Garba Kagara Wakilin ICPC da dai sauran su.

Kwamitin ya bayar da dama ga al’ummar da suke da Korafi da su shigar da korafe-korafen su a ofishin Sakataren Gwamnatin Jahar Kano kan abunda ya shafi yin tasiri da Filayen gwamnati, Makarantu da Makabartu bisa rashin bin ka’ida.

Kwamitin zai yi binciken ne tun daga shekarar 2015 zuwa 2023, na mulkin tsohuwar Gwamnatin Kano kamar yadda jaridar idongari.ng ta ruwaito.

Muna tafe da Karin bayani…………

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *