Kwamitin da IGP Kayode Adeolu, Ya kafa Ya gano Mutane 300 a gidan yarin Kano, wanda babu kundin laifukan da Suka aikata.

Spread the love

Kwamitin sanya ido kan aiyukan Yan sanda, Kotuna da gidan gyaran hali da tarbiya, ya gano wasu mutane 300 da ake tsare da su , shekaru ma su Yawa amma babu bayanan laifukan da ake zargin sun aikata.

Kwamitin Wanda Babban sufeton Yan sandan Nigeria IGP Kayode Adeolu Abegketun, ya kafa kuma ya umarci kwamishinonin Yan sandan jahohi, da su jagorancin kwamitin, ta Hanyar bibiya domin ganin an Yi wa dukkan dan Nigeria da ake tsare dashi a wajen Yan sanda ko kuma gidan yari adalci.

Kwamitin karkashn jogarancin Kwamishinan Yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ne ya kai ziyarar bazata a gidan gyaran hali da tarbiya dake Kurmawa a jahar Kano.

Za mu dauki mataki a kan masu tare motocinmu suna wawar kaya – NARTO

An kama ƴansintiri 10 kan zargin kashe limamin garin Mada

Daya daga cikin jami’an gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya na kurmawa, ya shaida wa kwamitin cewa babu kundin abinda ake zargin su da aikata wa .

Ya Kara da cewa, wasu daga cikin su babu hakikanin kotunan da za a Kai su , amma duk da haka sun shafe shekaru a gidan gyaran hali da tarbiya.

Daya daga cikin tsararrun ya bayyana wa kwamitin cewa, tun a shekarar 2009 aka tsare shi, kan zargin kisan Kai, amma har yanzu ba a taba gurfanar da shi a gaban kotu ba.

Haka zalika akwai wani mai suna Yahaya Usman Ikkara ta jahar Kaduna, Wanda aka tsare shi tun a shekarar 2017, kuma har Kawo yanzu bai San makomarsa ba.

Kwamishinan Yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya shaida wa Jaridar Idongari. ng, cewar, kwamitin dagaske yake wajen gudanar da aiyukan su, domin tabbatar da cewa mutanen jahar Kano su samu adalci kamar yadda kowanne dan kasa yakamata ya samu.

” Ba ma so muji an tsare mutum ba da hakki ba, ko kuma an tsare shi tsawon lokaci ba tare da an kaishi kotu ba, shi yasa kaga a cikin mu akwai Lauyoyi, kungiyar Kare hakkin dan Adam, Kungiyoyin al’umma, hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jahar Kano” CP Gumel “.

Tun a Ranar Talatar da ta gabata kwamitin ya Fara ziyatar ofishoshin Yan sanda hudu da Suka hada da Fagge, Zango, Shada da kuma Hotoro, sai kuma gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya na Janguza dake kan hanyar zuwa Gwarzo Kano.

A jiya Laraba kwamitin ya Fara ziyartar babbar Kotun jahar Kano dake miller Road , inda Suka gana da Alkalain kotunan.

Haka zalika sun ziyarci rukunin kotunan Majistiri Norman’Sland da Kotun shari’ar addinin musulinci mai lamba 1 dake Kofar Kudu Gidan Sarki Kano.

Daga bisani Yan kwamitin sanya idon sun karkare ziyarar ta su a gidan ajiya da yaran hali da tarbiya na Kurmawa Kano, inda aka gano tsaarrau kusan 300, wadanda babu kundin laifukan da ake zarginsu da aikata wa.

Kwamishinan Yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya ba wa tsararrun tabbacin cewar nan da makonni biyu za su dauki matakin da yakamata kan mutanen da ke tsare tsawon shekaru ba tare an gurfanar da su a gaban kotu ba.

Jaridar Idongari. ng, ta gano cewar , wasu daga cikin Tsararrun ana Kai su kotunan kasa ne, maimaokon manyan kotuna da kuma wadanda ko kotunan ba a Kai su ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *