Kwamitin Tsaron Da Gwamnatin Kano Ta Kafa  Ya Kai Sumame Tare Da Kama, Shanun Sata, Miyagun Kwayoyi Da Kuma Yan Daba 53.

Spread the love

 

Kwamitin tsaron da gwamnatin jihar Kano ta kafa don magance fadace-fadacen daba da ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma gyara tarbiyar matasa, ya kai sumame tare da kama matasa 53, a wuraren da aka samu rahotannin yan daba da masu sayar da kayan maye suna taruwa, don su fito fadan daba a cikin unguwannin kwaryar birnin Kano.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna kiyawa,ne ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce sun yi aikin ne cikin  kwanaki biyu da suka gabata, karkashin jagorancin shugaban kwamitin Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata, a unguwannin Yakasai, Kofar Mata, Zango, Zage, Kasuwar Rimi, Tashar Motar Shawuci , Dan Agundi, Sharada, Ja’en, Kano Line da makotan unguwannin da kuma Zanzado da ake zargin ita ce matattarar batagarin.

Kwamitin wanda gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kafa, ya ce an kama makamai da kayan maye da suka hada da, Tabar Wiwi sinki uku da kuma kulli-kulli guda 50, Codeine 2, Sholisho 1 da kuma Galan daya na madarar Sukudayin wato ( Suck & Die).

Sauran kayayyakin sune Adduna 5, Almakashi 2, Gorori 2, kwayar Exol  105, Layu da Guraye da kuma shanu 5 da kayan maye makare a cikin wata mota, a sumamen da aka kai Zanzado da ake zargin mallakar wani dilan kwaya da ake nema.

Kwamitin ya kara da cewa wadanda aka samu da makamai za a barwa jami’an yan sanda su don yin bincike, haka zalika wadanda aka samu da kayan maye kuma za a mika su hannun hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA don fadada bincike kafin a gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci

Kwamitin ya tabbatarwa da al’ummar jihar Kano cewa duk wanda ya fito ya ce al’ummar jihar Kano ba za su zauna lafiya ba, to tamkar ya gaiyatowa kansa ne fadan da bai shirya ba, domin ba za a barshi ba.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano , SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya kara da cewa gaba daya gamayyar jami’an tsaron Kano ne suka gudanar da aikin kuma an samu nasara babba, inda ya ce yanzu sun fara neman iyayen wadanda aka samu sunayensu yayansu da laifukan daba da kuma ta’ammali da miyagun kwayoyi don ganin an magance matasalar  baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *