Kwamitin Zaman Lafiya KPC Ya Yaba Wa Rundunar Yan sandan Kano Kan Kokarin Wanzar Da Zaman Lafiya A Dorayi.

Spread the love

Kwamitin Samar da zaman lafiya na jihar kano (KPC),ya yi Allah wadai da abun da wasu batagarin matasa suka yi, a unguwar Dorayi na yin fadan daba da sauran wasu manyan laifuka.

Wannan na kunshe ne a cikin wani sagon murya da shugaban kwamitin zaman lafiya na jihar Amb. Ibrahim Waiyya, ya raba wa manema labarai ta hannun mataimaki na Musamman kan kafafen yada labarai, Bashir A Bashir.

Kazalika Ambasada Ibrahim Waiyya, ya bayyana cewa kwamitin zaman lafiya na Kano na yaba wa rundunar yan sandan jihar kano, Karkashin Jagorancin, CP Muhammed Usaini Gumel, duba da irin kokarin da sukayi na samar da tsaro cikin gaggawa a yankin na Dorayi, tare da yadda aka samar da ofishin da zai yaki Yan Daba da Yan fashi da makami a yankin da kewayensa, harma da nasarar kama wasu dake da hannu wajen aikata laifi.

Daga karshe Kwamitin zaman lafiya na jihar , Kano Peace Committee ya yi kira ga sauran al’umma musamman na yankin Dorayi da su ci gaba da bawa Jami’an tsaro hadin kan da ya da ce, musamman wajen bayar da bayanin sirri domin samun nasarar da ake bukata na yaki da fadan daba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *