Kwastam Sun Kama Makaman N1.6bn A Filin Jirgin Legas

Spread the love

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama makamai da kudinsu ya haura Naira biliyan 1.6 a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Jihar Legas.

Makaman da aka kama sun hada da jirage marasa matuka da kakin soji da ragunan sulke da hulunan kwano da na’urorin sadarwa na oba-oba da sauran kayan yaki.

Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam na Kasa, Bashir Adewale Adeniyi, ya sanar cewa cikin makaman da aka kama akwai “bindigogi 55

 

sarrafa kansu kirar Jojef Magnum (Tomahawk) da kudinsu ya kai Naira miliyan 270.8.

“Bincikenmu ya gano cewa wasu ’yan Najeriya marasa kishi da ke zaune a kasar Turkiyya ne suka yi fasa-kwaurin makaman zuwa kasar nan.”

Ya kara da cewa an kama wani mutum da ake zargin hannunsa a shigowa da makaman da aka kama.

An yi wannan kamen ne a ranar Laraba, kimanin sa’o’i 48 bayan hukumar ta kama wata kwantaina makare da bindigogi 844 da harsasai 112,500 da aka yi fasa-kwaurin su zuwa Najeriya a tashar jiragen ruwa ta Onne a Jihar Ribas.

Shugaban kwastam na kasa ya bayyana cewa su ma makaman da aka kama a Jihar Ribas an yiwo fasa-kwaurinsu zuwa Najeriya ne daga kasar Turkiyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *