Kwastam ta kwace hodar iblis da kuɗinsa ya kai dala miliyan 150

Spread the love

Jami’an kwastam a Senegal sun ce sun kwace hodar iblis fiye da tan guda a kan iyakar kasar da Mali.

Sun ce wannan shi ne kwace mafi girma da ƙasar ta yi a kan kwaya.

An sanya hodar iblis ɗin a cikin leda aka kuma naɗe ta sannan aka saka a cikin wata babbar mota wadda aka tsayar da ita a kusa da garin Kidira.

An kiyasta kuɗin hodar iblis ɗin zai kai kusan dala miliyan 150.

Senegal na iyaka da ƙasashen da suka haɗ da Guinea da Mauritania da kuma Guinea Bissau wanda dukkansu sun yi fice a wajen da ake tsayawa da kwaya idan an ɗauko ta daga ƙasashen Latin Amurka da kuma Turai.

A watan Nuwamba, sojojin ƙasar ta Senegal suka bankaɗo kusan tan uku na hodar Iblis daga cikin wani jirgin ruwa a gaɓar ruwan ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *