Kwastam ta miƙa wa NDLEA tabar wiwi ta naira miliyan 371 da ta kama

Spread the love

Babban kwanturolan Hukumar Hana Fasa Ƙauri ta Najeriya da ke lura da filin jirgin sama na Legas, Michael Awe ya miƙa wa hukumar Hana sha da Fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA tabar wiwi ta kusan naira miliyan 371 da jami’ansa suka kama.

Cikin wani saƙo da hukumar Kwastam ta ƙasar ta wallafa a shafinta na X, ta ce jami’anta sun kama tabar ranar 17 ga watan Yuli ɗaure cikin wasu ƙwalaye 40 da aka yi yunƙurin safararta.

Hukumar ta ce ta kama mutumin da take zargi da safarar tabar inda shi ma ta hannunta shi ga hukumar ta NDLEA.

Kwanturolan ya ce hukumar za ta ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumar NDLEA domin kakkaɓe ayyukan masu fataucin miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *