Kwastam ta tabbatar da mutuwar mutane a turmutsitsin raba shinkafa

Spread the love

Hukumar kwastam a Najeriya ta tabbatar cewa turmutsutsin da aka yi a baya-bayan nan a cibiyar sayar da shinkafa a farashi mai rahusa ya janyo mutuwar mutane tare da jikkatar wasu.

Hukumar tana sayar da shinkafa ne kan farashi mai rahusa ga ƴan Najeriya daidai lokacin da farashin kayan masarufi ke ƙaruwa a sassan ƙasar.

A makon da ya gabata ne, kwastam ta ce za ta rarraba kayan abincin da ta ƙwace da ke ajiye a rumbunanta domin magance matsalar tsadar abinci a faɗin ƙasar.

Ana sayar da buhu mai mauyin kilogram 25 na shinkafar da aka ƙwace sakamakon haramcin shigo da ita daga wasu ƙasashen kan naira dubu goma abin da ya janyo dandazon mutane a wurin kasancewar ana sayar da irin buhun shinkafar kan naira dubu arba’in.

Yan sandan Kano sun gurfanar da mutane 9 Kan zargin sayar da Dala ba bisa ka’ida ba.

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Kamo Mawaki Ado Gwanja

Sai dai lamarin ya sauya bayan da jami’an kwastam suka faɗa wa taron jama’ar su sake komawa washegari saboda shinkafar ta ƙare.

Kwastam ta ce mutanen sun kutsa kai domin neman buhun shinkafa cikin kwantenonin da ba komai cikin su.

Ta ce lamarin ya janyo turmutsistin jama’a har ta kai ga mutuwar mutane da jikkatar wasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *