Labari cikin hotuna : Mataimakin sufeton yan sandan Nijeriya shiya ta daya dake Kano AIG Umar Mamman Sanda, ya ziyarci wajen tantance matasan da suka nemi shiga aiki yan sanda na 2022/2023.

Spread the love

Mataimakin sufeton yan sandan Nijeriya shiya ta daya dake Kano AIG Umar Mamman Sanda, ya ziyarci wajen da ake  ci gaba da tantance matasan da suka nemi shiga aiki yan sanda na 2022/2023.

AIG Umar Sanda, ya bayyana gamsuwarsa da abunda ya gane wa idonsa a wajen tantancewar.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce kwamishinan yan sandan jahar, CP Muhammed Usaini Gumel, ya bayyana cewa rundunar yan sandan Kanon, za ta ci gaba da bin dukkanin ka’idojin da aka gindaya bisa kwarewa a wajen tantancewar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *