Latsa Ka Kalli Wani Faifen Bidiyo Da Ya Nuna Yadda Tsoffin Sanatocin Kaduna Suka Ki Amince Wa Elrufa’i Ya Ci Wo Bashi , Har Ya Tsine Mu Su, Sannan Ya yi Amfani Da Sanata Uba Sani Wajen Ciyo Bashin.

Spread the love

Koda abaya tsohon gwamnan jahar Kaduna Mallam Nasir Elrufa’i, ya yi tofin Allah ya tsine ga sanatocin kadunan ukun, sakamakon kin amincewa da ciwo bashin da suka yi.

Nasir Elrufa’i, ya zargi sanatocin na baya kin amincewarsu, saboda basa so aci gaba da yi wa al’umma aikin hanya, asibiti, inda ya bayyana su , a matsayin makiyan talakawan Kaduna kamar Sule Hunkuyi, Shehu Sani da Danjuma Laah, Allah ya tsine musu, Allah ya mayar musu da aniyar su.” Inji El-Rufai.

Sai dai kuma su mambobi masu wakiltar Kaduna a majalisar Wakilai,sun sha yabo , daga gwamnan. El-Rufai kan kokarin da suka yi na ganin sun amince da wannan bashi da aka nema.

Suma wakilan majalisar dokoki na jihar sun sha wannan yabo.

Tun daga wancan lokacin ake ganin Elrufa’i ya yi amfani da gwamnan jahar na yanzu Sanata Uba Sani, wajen ciyo bashin da yanzu haka yake, kukan ya kasa biyan albashi saboda tullin bashin da aka ciyo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *