Lauyoyin Aminu Ado Bayero sun fice daga shari’ar dambarwar masarautu

Spread the love

Lauyoyin Sarkin Kano na goma sha biyar, Alhaji Aminu Ado Bayero, sun fice daga shari’ar dambarwar masarautar Kano wanda ake yi a babbar kotun jihar.

Lauyoyin sun ɗauki matakin ne a zaman da kotun ta yi ranar Alhamsi, bayan kai ruwa rana tsakanin ɓangarorin da ke shari’a da juna.

A lokacin zama kotun lauyan Aminu Ado Bayero, Abdul Muhammed, ya fara da shaida wa kotun cewa akwai takardar shaidar ta ke tabbatar da cewa sun ɗaukaka ƙara kuma an shigar da bayanan a gaban kotun, inda ya nemi kotun kada ta ci gaba da sauraron shari’ar har sai an saurari ɗaukaka ƙarar da suka yi.

Lauyan ya kuma buƙaci kotun ta ƙara musu lokaci don mayar da martani kan wasu takardu da ya ce an ba su ranar Laraba.

To sai dai ɓangaren masu ƙara sun soki waɗannan buƙatu, inda babban lauyan gwamnatin Kano da majalisar dokokin jihar, Eyitayo Fatogun ya ce babu waɗannan bayanan a kotun.

Inda ya shaida wa kotun cewa ba haka ake yi ba, yana mai cewa dokokin babbar kotu sun ce idan kana so ka shigar da wasu bayanai a gaban kotu nema ake yi ba kawai ka kawo wata takarda ba.

Bayan sauraron duka ɓangarorin biyu, Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta ce buƙatun da lauyan Aminu Ado Bayero ya gabatar ba su da karfin da za su hana ci gaba da sauraron shari’ar don haka ta yi watsi da su.

Inda ta bayar da umarnin ci gaba da sauraron shari’ar da ke gaban kotun

To sai dai wannan hukunci bai yi wa lauyoyin Aminu Ado Bayero daɗi ba, inda Barrister Sanusi Musa ya mike ya shaida wa kotun cewa sun fice daga wannan shari’a, sannan ya ce za su koma su sanar da wanda suke wakilta don ya nemi wanda zai wakilce shi, sannan suka fice daga kotun.

Bayan ficewarsu ne, kuma sai mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta ci gaba da sauraron karar, inda lauyan sarakunan da gwamnatin Kano ta ce ta sauke wato Bichi da Rano da Gaya da kuma Karaye, Hassan Tanko Kyaure ya buƙaci a ƙara masa lokaci don ya yi nazari akan takardun da aka ba su.

Sannan ya kuma buƙaci kotun ta rushe sabuwar dokar masarautun Kano ta 2024, amma mai shari’ar ta ce ba zai yiwu a ƙara musu lokaci ba, saboda ta bayar da odar cewa ba za ta ƙara lokaci ba.

Daga ƙarshe Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta ɗage zaman kotun zuwa ranar 18 wannan wata don yin hukunci a kan buƙatun da kowanne ɓangare ya nema.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *