Legas za ta hana amfani da robar tekawe daga gobe Litinin

Spread the love

Gwamnatin jihar Lagos ta ce daga gobe Litinin 19 ga watan Fabrairu za ta fara aiwatar da dokar haramta am fan I da robar sayar da abinci ta takway a fain jihar.

Kwamishin muhalli da albarkatun ruwa na jihar Lagos , Tokunbo Wahab, ne ya bayyana haka a lokacin ganawa da shugabannin kasuwannin jihar.

Haka kuma cikin wata sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar, Kunle Adeshina, ya fitar ranar Asabar, ya ce kwamishinan muhallin ya ce jami’an hukumar tsaftar muhalli da jami’an ‘yansanda da sauran hukumomin da lamarin ya saf za su zagaya kasuwanni domin kama robobin da ake sayarwa a shaguna.

Rundunar ’Yan Sandan Birnin Tarayya, sun kai farmaki tare da kashe wasu kasurguman ’yan bindiga.

Yansanda sun kama mutum takwas da suke zargi da sace ɗaliban Ekiti

Sanarwar ta yi kira ga ‘yan kasuwa da su guji sayar da abinci a kan layukan dogo da titunan mota.

”Dole ne mu tsftace kasuwanninmu daga abin da zai guata mana ita”, in ji kwamishinan.

Ya ƙara da cewa dole a raba shara daga kasuwannin jihar, do inganta lafiyar al’umma

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *