Libya Ta Mayar Da Bakin Haure 369 Daga Najeriya Da Mali Zuwa Gida

Spread the love

Wani jami’i ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar, a yau Talata kasar Libya ta mayar da bakin haure 369 zuwa kasashensu na asali; Najeriya da Mali ciki harda mata da yara kanana fiye da 100

Wani shugaba a ma’aikatar cikin gida ta Libya, Muhammad Baredaa, da aka dorawa alhakin yaki da kwararowar bakin haure, jiragen sama 2 suka yi jigilar maida bakin haure 204 zuwa Najeriya sannan 165 zuwa kasar Mali.

A cewar Beradaa, bakin hauren da aka mayar Najeriya sun hada da jarirai 9 da kananan yara 18 da mata 108.

Ya kara da cewar an yi jigilar mayar da bakin hauren ne da hadin gwiwar Hukumar IOM, mai kula da masu kaura ta Majalisar Dinkin Duniya.

Hukumar ta IOM ke samar da jigilar jiragen sama kyauta ga bakin hauren tare da taimaka musu wajen sake komawa cikin danginsu a kasashensu na asali karkashin shirinta na “aikin jin kai na mayar da bakin haure gida”.

Sai dai wasu daga cikin bakin hauren sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa da karfin tsiya ake kokarin mayar dasu gida.

Hakim dan Najeriya ne mai shekaru 59 da haihuwa, wanda ya rayu a kasar Libya tsawon shekaru 25 kuma yaki yarda ya bayyana sunan mahaifinsa yace, “da tsakar dare hukumomin libya suka balle mana kofa.

Ya kara da cewa “sai da suka karbe mana takardun tafiye-tafiye kafin su tsare ni da mai dakina gabanin taso keyarmu zuwa gida”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *