Ƙungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta fara yajin aikin gargadi na kwana bakwai a dukkanin cibiyoyinta na faɗin ƙasar, inda ta buƙaci a sako Dakta Ganiyat Popoola, mambarsa da ke hannun masu garkuwa da mutane tsawon wata takwas.
Shugaban NARD, Dakta Dele Abdullahi ne ya sanar da fara yajin aikin a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya bayyana cewa za a fara yajin aikin da ƙarfe 12:00 na safe a ranar Litinin 26 ga watan Agusta, 2024.
An yanke shawarar yajin aikin ne a wani taron gaggawa da jagororin ƙungiyar suka gudanar a ranar Lahadi, 25 ga Agusta, 2024.
An sace Dokta Ganiyat Popoola, magatakarda a sashin kula da ido da ke Babban Asitin Ido na ƙasa da ke Kaduna ne, kusan wata 8 da suka gabata, tare da mijinta da kuma ɗan uwanta.
Sai dai an saki mijinta a watan Maris, amma aka ci gaba da riƙe Popoola da dan uwanta.
Makonni da suka gabata, mambobin NARD sun yi zanga-zanga a dukkan manyan asibitocin ƙasar, don neman a gaggauta sakinta.