Kungiyar ma su hakan Kabari reshen jahar Kano, ta yi kira da gwamnatin jahar ta fara biyan Alawus duk wata, biyo bayan sauyin rayuwa da matsin tattalin arziki da talakawan Nigeria suka fada sakamakon sauye-sauyen da gwamnatin tarayya ta yi.
Shugaban kungiyar reshen jahar Kano Mallam Muhammad Inuwa Abubakar, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gana wa da jaridar Idongari.ng a jiya Lahadi.
Mallam Muhammad ya ce sun kafa kungiyar ce domin taimakon junansu, amma sakamakon rashin babu da yayan kungiyar suka tsinci kansu a ciki har huluna suke rike wa suna neman taimako a duk lokacin da ake binne mamaci.
EFCC ta ƙwato naira biliyan 60 a cikin kwana 100 – Olukoyede
Ƙungiyar sanatocin Arewacin Najeriya za ta tura tawaga Nijar
Ya kara da cewa ma su hakan kabarin sun ce tun da safiya suke zuwa cikin makabarta har bayan sallar Isha’I.
‘’ Gwamnatin jahar Kano ta yi hobbasa wajen tallafa wa masu hakan kabari’’.
A karshe ya yi fatan ma su hannu da shuni da suma za su, sanya hannun su wajen tallafa mu su, sakamakon ba su da wata sana’a da ta ke fice hakan kabari.