Ma Su Magana Da Yawun Yan Sandan Jahohin Arewa Maso Yammacin Nigeria Sun Halacci Taron Kara Wa Juna Sani A Abuja.

Spread the love

Gamayyar ma su magana da yawun rundunar yan sandan Nigeria, shiyar arewacin kasar , sun halacci taron kara wa juna  sani a babbar cibiyar nan ta National Institute of Police Studies Abuja.

Jagoran ma su magana da yawun rundunar yan sandan Nigeria mai kula da shiya ta 14 da ya hadar Katsina da Kaduna CSP Gambo isah, ne ya bayyya hakan a madadin sauran abokan aikin sa na jahohin arewa maso yammacin Nijeriya.

CSP Gambo Isah, ya ce sunje birnin tarayya Abuja ne domin kara wa juna ilimi da kuma bitar da suka samu tare da gaisa wa da juna don kara dankon zumunci a tsakaninsu.

Jaridar Idongari.ng, ta ruwaito cewa dukkan jami’an da suka halacci taron bitar sun kasance cikin annushuwa, a cikin wani faifen bidiyo da kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa,  ya wallafa a shafin sa na Facebook da yammacin ranar Talata.

Wadanda suka halacci taron bitar sun hada da CSP Gambo Isah daga rundunar yan sandan Nigeria shiya ta 14 Katsina da Kaduna, CSP Bashir Muhd daga shiya ta 1 Kano da Jigawa, ASP Usman Yakubu Muhammed daga ta 10 Sokoto, Kebbi da kuma jahar Zamfara.

Sauran sun hada da kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullhi Haruna Kiyawa , da mai magana da yawun yan sandan jahar Kebbi SP Nafi’u Abubakar, kakakin yan sandan jahar Jigawa DSP Shiisu Lawan Adamu, kakakin yan sandan jahar Kaduna ASP Mansur Hassan, kakakin yan sandan jahar Zamfara ASP Yazid Abubakar, kakakin yan sandan jahar Sokoto ASP Ahmed Rafa’i da kuma kakakin yan sandan jahar Katsina ASP Abubakar Sadik Aliyu.

Ga jerin sunayen su.

PPRO Zone 14  Katsina & Kaduna, CSP Gambo Isah.

PPRO Zone 1 Kano & Jigawa CSP Bashir Muhd.

PPRO Kano State SP Abdullahi Haruna Kiyawa.

PPRO Kebbi State SP Nafi’u Abubakar.

PPRO Jigawa State DSP Shiisu Lawan Adamu.

PPRO Zone 10, Sokoto, kebbi & Zamfara ASP Usman Yakubu Mohd.

PPRO Katsina State ASP Abubakar Aliyu Sadik.

PPRO Sokoto State ASP Ahmed Rufa’i.

PPRO Zamfara State ASP Yazid Abubakar.

PPRO Kaduna State ASP Mansur Hassan.

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *