Kamfanin Binance ya tabbatar wa BBC cewa ɗaya daga cikin jami’ansa da hukumomin Najeriya suka tsare, a yanzu ba ya hannu daidai lokacin da ake yaɗa rahotannin cewa ya tsere daga Najeriya.
Nadeem Anjarwalla, wanda ke da fasfon ƙasashen Birtaniya da Kenya, an kama shi ne a cikin watan jiya tare da abokin aikinsa, Tigran Gambaryan, a wani ɓangare na binciken kaucewa biyan haraji da gwamnatin Najeriya ke yi wa kamfanin na kudin kirifto.
Kakakin Binance ya ce “mun samu labarin cewa Nadeem ba ya hannun Najeriya. Babban abin da muka mayar da hankali a kai shi ne tsaron ma’aikatanmu kuma muna aiki tare da hukumomin Najeriya domin warware batun ba tare da ɓata lokaci ba.”
Har yanzu dai hukumomin Najeriyar ba su ce komai ba a game da haka.
- Harkar Noma Ce Kaɗai Za Ta Samar Da Zaman Lafiya A Najeriya — Peter Obi
- Kotu Ta Haramta Wa Murja Kunya Amfani Da Soshiyal Midiya
Tuni dai gwamnatin Najeriya ta maka kamfanin a gaban kotu inda ta shigar da tuhume-tuhume guda huɗu a kansa da suka shafi ƙin biyan haraji.
Babban bankin ƙasar ya yi zargin cewa fiye da dala miliyan 26 ne ake hada-hadar su a kasuwar hada-hadar kudin kirifto ta Binance.
Ya kuma zargi shafin da saka wa dala farashi abin da ke ƙara janyo karyewar darajar naira.