Ƙungiyar ƙwadago ta NLC rehen jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta sanar da shirin ma’aikatan jihar na tsunduma yajin aiki nan da ƙarshen wannan wata na Nuwamba, muddin gwamnatin jihar ba ta fara biyan sabon albashi mafi ƙaranci na naira dubu saba’in ba.
Ƙungiyar ta ce matakin jan ƙafar na nuna yadda wasu gwamnonin jihohi ba su jin tausayin ma’aikata musamman a wannan lokaci da al’umma ke fama da tsadar rayuwa.
Gwamnatin Zamfara dai ta sanar da amincewa da naira dubu 70 ne a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan jihar.