Ma’aikatan jami’a za su yi zanga-zanga a faɗin Najeriya

Spread the love

Ƙungiyar manyan ma’aikatan jami’a a Najeriya ta Senior Staff Association of Nigerian Universities (SSANU) ta yi barazanar shiga yajin aiki faɗin ƙasar.

Kazalika, ƙungiyar ta ce za ta gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya a ranar Talata mai zuwa domin matsa wa gwamnatin tarayya ta biya mata buƙatunta.

Ƙaungiyar da takwararta Non-Academic Staff Union of Educational and Associated Institutions (NASU) na tattaunawa da gwamnatin Najeriya game da albashinsu na wata huɗu da suke bin ta, wanda yanzu ta ba da wa’adin mako biyu domin biyan mambobinta.

“A matsayinmu na shugabanni, mun yanke shawarar zuwa Talata 9 ga watan Yuli rassanmu za su shirya zanga-zanga a ƙasa baki daya domin faɗa wa duniya irin matsalolin da ake fuskanta, kuma za a yi a dukkan makarantu,” in ji shugaban SSANU Mohammed Ibrahim yayin hirarasa da Channels TV a yau Juma’a.

Ya ƙara da cewa “daga baya kuma za mu ci gaba da tattaunawa, sai kuma mu sake yin babbar zanga-zanga a Abuja ranar 18 ga watan Yuli, inda za mu yi wa ma’aikatun ilimi da ƙwadago tsinke”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *