Ma’aikatan jami’o’in Najeriya sun janye yajin aiki

Spread the love

Ƙungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya (SSANU) da ƙungiyar da ba ta malamai ba (NASU) sun janye yajin aikin gama-gari da suka soma a faɗin ƙasar.

Ƙungiyar ta sanar da batun janye yajin aikin ne yau Lahadi a wata sanarwa da shugabanta Mohammed Ibrahim ya fitar, inda ya umarci dukkan mambobin SSANU da NASU da su koma bakin aiki a ranar Litinin, 25 ga watan Maris.

SSANU da NASU sun tsunduma yajin aiki ne a makon da ya gabata domin nuna rashin amincewarsu da abin da suka ɗauka a matsayin rashin adalci da kuma saɓani na biyan albashi da gwamnatin tarayya ke yi.

Sun kuma zargi gwamnatin tarayya da yin zagon kasa musamman wajen rashin biyansu kamar da ake yi wa takwarorinsu malamai.

Ƙungiyar ta tabbatar wa mambobinta cewa za su ci gaba da gwagwarmaya har sai gwamnati ta biya su kuɗaɗen da suke bin ta.

Ta kuma yi alkawarin cewa za su ci gaba da tattaunawa da hukumomin gwamnati da suka kamata da kuma sanarwa mambobinsu mataki na gaba da za su ɗauka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *