Ma’aikatar Tsaron Najeriya Ta Mika Sabbin Jiragen Saman Shelkwafta Ga Rundunar Sojin Ruwa

Spread the love

Ma’aikatar tsaron Najeriya ta mika jirgen saman shelkwafta 3 kirar Agusta Westland 109 ga rundunar sojin ruwan kasar.

Sanarwar da daraktan yada labaran rundunar sojin ruwan, Commodore A. Adams-Aliyu, ya fitar a yau Laraba, tace kwarya-kwaryan bikin mika jiragen ya gudana ne a wurin adana jiragen shelkwafta mallakin kamfanin Caverton dake yankin Ikeja, a jihar Legas.

An yiwa jiragen saman shelkwaftar AW 109 kirar alfarma da kujerun fata da tsarin takaita kara, a cewar sanarwar.

Babban Hafsan Sojan Ruwan Najeriya, Vice Admiral Emmanuel Ogalla, a bisa rakiyar manyan dakarunsa sun halarci bikin karbar sabbin jiragen saman shelkwaftar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *