Ma’aikatar yada labarai ta jihar Kano, tare da hadin gwiwar NEXA, sun shirya taron horas wa na wuni biyu ga wadanda suke yada manufofi da aiyukan gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, a shafukan sada zumuntar, Facebook, X, Tiktok, Instergram, dabarun yadda za su yi amfani da shafukan ta hanyar bin dokoki da kuma tantance labaran karya don tsaftace harkar baki daya.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa sun gayyaci kwararru don horas da matasan da suka gayyata kan yadda za su kaucewa cin mutuncin mutane a shafukan sada zumunta.
Waiya ya kara da cewa, daman suna wani zaure na ma’abota shafukan sada zumunta don yada aiyukan gwamnatin Kano, inda suka dacewar hadasu wuri guda don horaswa da su dabarun yadda yakamata su gudanar da aiyukansu.
- An kama ɗan daba mai yin fashi a cikin shigar mata a Kano
- Human Rights Commission Lauds Kano Police Efforts, Explores Partnership Opportunities
‘’ za mu koyar da su yadda ake amfani da shafukan sada zumunta da kuma yadda zaka samar da labari na gaskiya don isarwa ga al’umma da kuma kaucewa yada labaran karya’’ Waiya’’.
Ya ce suna fatan bayan kammala samun horon na wuni biyu za sus amu kwarewa kan wadda suke da ita don inganta aikinsu wajen kawo rahotannin aiyukan gwamnatin Kano.
Wasu daga cikin mahalatta bitar sun bayyana gamsuwarsu kan horaswar, tare da cewa zai kara tsaftace harkar musamman yadda ake samun wasu suna cin mutuncin mutane a shafukan sada zumunta.
Taron dai an gudanar da shi ne a sabuwar jami’ar Bayero Kano, inda ya samu halattar jama’a daga sassa daban-daban.





