Hukumar zaɓe a Venezuela ta ce shugaba Nicolas Maduro ya lashe zaɓen ƙasar a wa’adin shugabanci na uku duk da koken yan’adawa an yi aringizon ƙuri’u a zaɓen na ranar Lahadi.
Wakiliyar BBC ta ce shugaban hukumar zaɓen ƙasar ya ce an ƙidaya kashi 80 na ƙuri’u, kuma Mr Maduro ya samu ƙuri’u miliyan biyar inda abokin hamayyarsa Edmundo Gonzalez ya samu kusan miliyan huɗu.
Ƴan adawa sun ce ana hana wakilansu shiga wurin ƙidayar ƙuri’u, kuma ba a ba su damar ganin takardun zaɓen ba.
Sai dai gwamnatin Venezuela ta ce sahihin zaɓe aka gudanar.