Innalillahi wa’innailaihi raji’un
Allah ya yi wa Hajiya Laurat Ibrahim Koki, mahaifiyar Hon. Engr, Sagir Ibrahim Koki, dan tarayya a karamar hukumar birnin Kano rasuwa.
Hajiya Laurat ta rasu ta na da shekaru 94 a duniya, kamar yadda aminin dan majalissar Alhaji Aminu Sa’id Adhama, ya tabbatar wa da jaridar idongari.ng.
Za a yi janazar marigayiyar a ranar laraba 19-6-2024 a masallacin Alhassan Dantata Koki da misalin karfe 9:00am a birnin Kano.
Allah ya yi mata rahma amin.