Mahaifiyar Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, Hajiya Maryam Namadi Umar ta rasu.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan, Hamisu Mohammed Gumel ya fitar, inda ya ce mahaifiyar gwamnan ta rasu ne a ranar Laraba, 25 ga Disamban 2024.
Sanarwar ta ƙara da cewa za a jana’izarta ne da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a Kafin Hausa.
- Kotu Ta Sauya Ranar Yanke Hukunci Ga Matashin Da Ake Tuhuma Da Laifin Cinnawa Masallata Wuta A Kano.