Rundunar yan sandan jahar Kano, ta nuna alhininta dangane da rasuwar Hajia Hauwa Umar Chusu, mahaifiya ga mukaddashin kwamishinan yan sandan jahar, DCP Umar Ahmed Chusu.
Hajia Hauwa Umar, ta rasu ne ta na shekaru 75 a duniya.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar litinin 7 ga watan Oktoba 2024.
Sanarwar ta ce a madadin kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, da kuma sauran jami’an rundunar, suna mika ta’aziyarsu ga DCP Umar Chusu da yan uwansa bisa rashin marigayiyar.
Rundunar ta yi addu’ar Allah ya yi mata rahma, ya sa aljannatul Firdaus ce makoma.
- Mataimakin shugaban ƙasar Kenya zai gurfana gaban majalisa
- Ban Ji Dadi Ba Da Tinubu Ya Ambaci Sunana Ni Kadai – Fubara
Al’umma da dama sun mika sakon ta’aziyarsu a wallafar da kakakin rundunar yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, Ya yi a shafin sa na Facebook
Hamisu Aliyu Subuhanallahi wabihamdihi Innalillahi wainailaihirrajiun Allah ya jikanta da rahama accept My condolences pls
Salim Candy Allah ya mata Rahama.
Zainab Nasir AhmadAllah ubangiji ya gafarta mata
Ahmad Wada Nadada Allah ubangiji ya gafarta mata
Mujahid Wada Gurungawa Kano Allah ya yi mata rahma
Abban Dabarani Tarda Allahu Akbar ubangiji yajadda rahama agareta yasa Aljanna ce makomarta yabada hakuri
Musa Mhd Zakariyya Allah sarki rayuwa kenan.Allah ya kar6i baquncinta.ya yafe kurakuranta Iyalanta kuma Allah ya basu haqurin jure rashin.
Usman Hossain Abdullahi May Allah grant her jannatul fiddaus . Ameen , Allah ya gafarta mata
Itzussy Kano Allah yajikanta da Rahma yasa aljannah firdausi makoma shi kuma Allah ya bashi hakurin jure rashin ta
It’z Amir Ahmad Danhassan Allah yajikan tah da rahama yasa aljannah firdausy makoma a gareta Allahummah Ameen