Babbar mataimakiya ga gwamnan jahar kano, kan ilimin yaya mata, Hajiya Hafsat Adhama, ta bayar da da kayan karatau na yara yan makaranta ga zababben shugaban karamar hukumar , Gwale Hon. Abubakar Ma’azu Mojo, guda 40 na maza da na mata , tare da kayan karatu da suka hada da Jakunkuna, fensirl da kuma Littattafai da dai sauran su.
Hajiya Hafsat Adhama ta kasance mace mai kamar maza kuma mai kishi da tausayin yaran talakawa, tunda Gwamnan Kano ya bata wannan mukami bata zauna ba, kullum tana fafutukar yadda zata ga yaran talakawa sun yi karatu, cikin tsafta da walwala Hatta wanda basa zuwa makaranta burinta taga suna sun fara zuwa makaranta.
Yana daga cikin abinda shugaban karamar hukumar Gwale yake kokari akai na ganin an taimakawa yaran da basa zuwa makaranta don suma suna koma makaranta.
Haka zalika ta girmama shugaban karamar hukumar bisa ga yadda yake bata gudunmawa akan wannan kokari nata na ganin yaran talakawa sun koma makaranta tare da bata dikkan gudunmawar da ta dace.
- SEDSAC ta Yabawa Gwamnan Kano Bisa Nadin WaIya Da Iro Ma’aji A Matsayin Kwamishinoni
- Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutane 10 A Wajen Rabon Tallafin Abinci A Abuja