Mai Girma Gwamna ka shiga lamarin mu a matsayin mu na kanana da matsakaitan yan kasuwar Abubakar Rimi ta Sabon gari.

Spread the love

Hadaddiyar Kungiyar kanana da matsakaitan yan kasuwar Abubakar rimi ta sabon gari dake nan kano sun bukaci Mahukunta musamman gwamnatin kano da tayi iyakar kokarin ta wajen kwatar musu hakkin su a wajen wasu mutane da Gwamnatin baya ta Mallaka musu gurin da ‘yan kasuwar suke Neman Abincin su sama da mutane Dubu biyar.

Sakataren kungiyar kanana da matsakaitan yan kasuwar Sabon gari, Kabiru Sani Me Arsenal ne yayi kiran yayin wata zantawa da wakilin mu a yammacin ranar Talata Jim kadan bayan mika korafin Nasu a rubuce wajen Kwamishinan ma’aikatar harkokin kasuwanci na kano Gwani Shehu Wada Sagagi.

Sani Kabiru yace, sun rubuta korafin su tun zamanin tsohuwar gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje, yayin da Abbas Sani Abbas ke a matsayin Kwamishinan ma’aikatar harkokin kasuwanci da Chinikayya ta kano amma ba’a kira su anji daga garesu ba har wa’adin gwamnatin ya kare.

Wanda yace “Munga dacewar mu sake rubuta korafin mu domin mu sake mika wa Kwamishina Shehu Wada Sagagi domin bincike tare da daukar matakin da ya dace” *_a cewar Sani Kabiru me Arsenal_*.

Ya kara da cewar, tun a baya sun shigar da kara kotu akan yanda suke zargin tsohuwar gwamnatin Ganduje ta mallakawa wani mutum 1, sakamakon Alkawarin da tayi musu akan za tayi Ginin zamani a wajen bisa Alkawarin zata basu kasan Benen ta dauki saman, amma hakan bai samu ba, shine Dalilin shigar da kara kotu. Inji Sakataren Kungiyar kanana da matsakaitan yan kasuwar Sabon gari Sani Kabiru me arsenal.

Hakan ne tasa kotun ta bayar da Umarnin dakatar da duk wani aiki a cikin ginin da akeyi na zamanantar da wajen da aka kori wadannan yan kasuwa kamar yanda muka jiyo Umarnin kotun daga bakin Alkalin Babbar kotun jiha me lamba 26 dake zaman ta a Karamar hukumar Gaya Wanda Muma muka samu kwafin Umarnin (Court order) yayin zaman kotun da ya wakana a karamar hukumar ta Gaya.

A nasa bangaren Ma’ajin kudin kungiyar kanana da matsakaitan yan kasuwar Abubakar Rimi ta Sabon gari Abdul aziz Muhammad, yace Babban burin su bai wuce suga gwamnatin kano ta dawo dasu inda suke gudanar da Sana’ar su ba, ko Kuma ta Mallaka musu gurin da suke ta faman kai komo a kansa ba.

Inda yace, sun kai korafin su ga Manajan Daraktan Hukumar gudanarwar kasuwar Hon Abdul Hussain amma yace wai “Lamarin yafi karfin sa, Wanda yanzu haka kanana da matsakaitan yan kasuwar Sabon gari suna cikin wani hali na rashin tabbas akan Jarin da suke juyawa sakamakon yanda suke samun karyewar tattalin arzikin kasuwancin su, Wanda kuma ba haka ake so ba a matsayin jihar kano ce Cibiyar kasuwanci a duk fadin kasar nan. Inji Abdul Aziz Muhammad.

A karshe sunyi fatan gwamnatin kano zata duba koken su, ta kuma kawo musu daukin da ya dace

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *