Mai Martaba Sarkin Kano Na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero Ya Bukaci Masu Rike Wata Dama Su Taimakawa jama’arsu

Spread the love

Mai martaba sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci masu rike da wata dama da su yi kokarin taimakawa jama’arsu.

Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana hakan ne lokacin da yake gabatar da jawabinsa, a wajen bude makarantar Lum’ul Hidayati Primary & Islamiyya School, wadda Kachallan Kano Hon. Ahmad Ibrahim Yakasai, ya gina a matsayin Wakafi ga mahaifiyarsa Marigayiya Hajiya Asma’u Ibrahim Yakasai.

Wannan nada dada cikin aiyukan alkairi da Kachallan Kano Hon. Ahmad Ibrahim Yakasai, kuma jakada na musamman a kasar Pakistan ke yi ga al’umma a bangarori dabam-daban.

Sarkin ya godewa Kachallan Kanon da kuma dukkan wadanda suka taimakawa wajen kammaluwar aikin tare da addu’ar Allah ya kai ladan ga wadda aka yi domin ta.

Haka zalika ya yi kira ga jama’a su mayar da hankali wajen kyautatawa wadanda ake tare da su , musamman ga wadanda Allah ya bawa wabi mikami ko sarauta ko arziki baya bashi ne domin yafi kowa wayo ba, Allah ya bashi ne domin ya taimakawa wadanda bai basu dama ba.

‘’ Yadda wanda ya gina wannan makaranta shima Allah ya faranta masa kuma Allah ya faranta muku’’ Sarkin Kano na 15’’.

A karshe mai martaba sarkin Kanon na 15 na godewa jami’an tsaro da mutanen da suka yi masa rakiya har zuwa wajen taro, tare da yin addu’a samun zaman lafiya da damuna mai albarka.

Anasa bangaren, Kachallan Kano Hon. Ahmad Ibrahim Yakasai, kuma jakada na musamman a kasar Pakistan, ya bayyana cewa wannan rana ce ta alhini a gareshi saboda a ranar 4 ga watan oktoba ya yi rashin mahaifiyarsa tare da yin farin cikin yadda Allah ya nufe shi da gina wakafi na mahaifinsa tu a shekarar 2006 sannan ya gina na mahaifiyarsa a wannan shekara ta 2025.

Ya kuma ce yayi ne badon alfahari ba, domin tun abaya na nunawa mutane muhimmancin wakafi ga mutane su gina tun suna raye ba sai sun mutu ba.

Kachallan Kanon ya kara da cewa tun kafin gina wajen an samar da rijistar cewa koda ya rasu babu wanda zai ci gadonsa, kuma duk wata shi ne yake biyan malaman makarantar albashinsu.

‘’ ina mai tabbatar maka indai ina raye ban gajiya ba zan ci gaba da taimakawa’’.

Kaza lika ya godewa al’ummar da suka taimaka wajen kammala ginin makarantar ta hanyar kawo buhunan siminti da bula da kudi da dai sauransu.

A karshe ya ce yana alfahari da iyayensa , tare da yin kira ga wadanda iyayensu suke raye da su dinga taimakawa iyayensu da kuma yin biyayya don samun albarka.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *